NAHCON ta aikewa Saudiyya wasika kan hana ‘yan Najeriya biza

0
218

Hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce ta rubutawa Saudiyya a hukumance, inda ta sanar da ita halin da ake ciki game da ƙarancin biza ga ‘yan ƙasar da suke son zuwa umrah.

NAHCON ɗin ta ce ta yi wa hukumomin Saudiyyar bayanin illar rashin bai wa kamfanonin shirya tafiye-tafiyen bizar a yanayin da ake ciki.

Cikin wata sanarwa da hukumar NAHCON ta fitar ta bayyana irin kalubalen da ‘yan Najeriya ke fama wajen samun bizar shiga saudiyya don gudanar da ibadar umrah a wanann wata na Ramadan a matsayin abin takaici.

Dumbin maniyyata wadanda suka shirya tafiya umrah tuntuni tsakaninsu da kamfanonin shirya tafiye-tafiye, suna ci gaba da bayyana takaicinsu da rashin samun biza daga hukumomin Saudiyya.

Adadin masu zuwa Umrah a lokacin watan Ramadan galibi ya kan fi na sauran lokuta saboda kwadayin dacewa da tarin ladan da ke tattare da yin ibadar a cikin watan na azumi, inda miliyoyin musulmi daga kasashe da dama na duniya ke zuwa yin umarah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here