CBN na neman yan Najeriyar da suka ci bashinsa fiye da naira biliyan 260

0
202

Babban bankin Najeriya wato CBN ya ce har yanzu wasu ‘yan kasar da suka akrbi bashinsa lokacin annobar korona ba biya ba.

A wani rahoto, babban bankin na Najeriya ya ce yana bin mutanen fiye da naira biliyan 260.

Babban bankin na Najeriya ya ce daga cikin naira biliyan 419.42 da bankin ya fitar domin bayar da rancen, naira biliyan 41 da miliyan 39 ne kawai jama’a suka biya, inda kuma aka samu kudin ruwa na naira miliyan 174 da dubu 600.

Kuma abin da hakan ke nufi shi ne akwai fite da naira biliyan 378 da mafiya yawan wadanda suka ci bashin ba su biya ba.

Rahoton ya kara da cewa kowane mutum daga cikin wadanda suka ci bashin, ya amfana da naira miliyan biyu da rabi.

Dangane kuma da fa’aidar da rancen ya yi ga wadanda suka ci gajiyarsa, bankin ya ce shirin, ya samar da ayyukan yi fiye da miliyan daya da rabi a fadin Najeriya.

Bayan annobar Korona ne dai gwamnatin Najeriya ta hanyar babban bankin kasar, ta fitar da makudan kudade domin bai wa ‘yan kasar rance kasancewar sana’ao’i da jari sun lalace a lokacin kullen annobar.

An kuma aiwatar da Shirin ne ta hanyar bankin bayar da rance ga masu kanana da matsakaitan sana’ao’i na NIRSAL.

To sai dai kuma a daidai lokacin da babban bankin ke son a kawo karshen shirin yanzu, fiye da rabin kudaden sa makale a hannun wadanda suka ci bashin.

To a amma rahoton babban bankin ya bayar da shawarar cewa za a iya karkata akalar Shirin ta koma karkashin Shirin kanana da matsakaitan sana’ao’i masu alaka da noma domin cigaba da shirin a kuma tabbatar da cewa jama’a sun biya kudaden ko da bayan kammala Shirin ne.

Masana tattalin arziki da masu lura da al’amura dai na ganin beken babban bankin, kasancewar a lokacin da ya bayar da rancen bai yi wa al’ummar kasar cikakken bayanin cewa kudin rance ne ba kyauta ba.

Harwayau, kasancewar wadanda suka ci gajaiyar sun yi hakan ne ta hanyar wasu shugabannin siyasa, ya sa mutanen suka yi tunanin kudin na bulun ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here