Yadda El-Rufai ya tarawa Kaduna bashi mai yawan gaske – Uba Sani

0
211

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin da dala miliyan 587 da bashin Naira biliyan 85 da kuma ayyukan kwangila 115 daga gwamnatin Nasir El-Rufai.

Gwamna Sani ya koka kan tashin farashin canji, wanda ya ce jihar na biyan kusan ninki uku na bashin da gwamnatin baya ta karbo.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a Kaduna a ranar Asabar yayin da yake jawabi a wajen wani taro, inda ya ce dimbin bashin da ake bin jihar na laƙume abin da jihar ke samu.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan bakwai daga cikin Naira 10 da Gwamnatin Tarayya ta ware mata a watan Maris, domin biyan bashi.

Gwamnan ya koka da yadda gwamnatin El-Rufai ta bar wa jihar biliyan uku kacal a asusun jihar, wanda ya gaza biyan albashin ma’aikata da ake biya na Naira biliyan 5.2 a duk wata.

Gwamna Sani, ya ce gwamnatinsa ba ta ci bashin ko sisi ba tun bayan wata tara da ya hau mulki, duk da dimbin bashin da ya gada.

“Duk da dimbin bashin da ya kai na dala miliyan 587 da na Naira biliyan 85, da kuma bashin ayyukan kwangila 115 da muka gada daga gwamnatin baya, amma mun ci gaba da jajicerwa wajen ganin Jihar Kaduna ta samu ayyukan ci gaba.

“Mun yi nazari cikin tsanaki kan halin da muke ciki. Ina sanar da ku cewa duk da dimbin bashin da muka gada, har zuwa yanzu ba mu ciyo bashin ko kobo ba,” in ji shi.

Gwamnan ya kara da cewa muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba sun hada da tsaro, samar da gidaje, ilimi, kiwon lafiya, da tallafa wa masu kananan sana’o’i.

Ya ce gwamnatinsa za ta kuma mayar da hankali wajen samar da ci gaba ta hanyar saka hannun jari, inganta tattalin arziki da samar da gidaje masu sauki.

Gwamna Sani, ya bayyana wasu muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba a 2024 da suka haɗar da tsaro, samar da ababen more rayuwa, bunkasa ilimi, samar da gidaje da ci gaban birane da dai sauransu.

A nasa jawabin, tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya bukaci a ɓullo da hanyoyin magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, inda ya ce idan ba a samu zaman lafiya da tsaro, ba za a iya samun ci gaban da jihar ke muradi ba.

Ya yaba wa gwamnan kan yadda ya rage hanyoyin da kuɗaɗen tafiyar da gwamnati ke zurarewa.

Ya bukaci al’ummar jihar da su guji nuna bambancin siyasa, addini ko kabilanci tare da mara wa gwamnatin jihar baya domin shawo kan kalubalen bashi da ta ke fuskanta.

Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamali, ya yi wa gwamnatin fatan alheri duk da kalubalen da ta ke fuskanta.

Ya kuma kara da cewa gwamnan yana da gogewar da zai inganta tattalin arzikin jihar domin samun ci gaba.

Ya kuma yi alkawarin mara wa gwamnatin baya ta hanyar haɗa kan masu sarautar gargajiya a jihar domin ganin gwamnatin ta yi nasara.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here