Wasu mazaunan jihar Kebbi sun auka cikin wani gidan ajiyar kaya na gwamnati a unguwar Bayan Kara cikin Birnin Kebbi, inda suka wawashe buhunhunan kayan abincin da ke ciki.
Mutanen waɗanda suka bijire wa jami’an tsaron da aka jibge a gidan ajiyar, sun kuma fasa wasu gidajen ajiyar kaya na ‘yan kasuwa da shagunan da ke yankin inda suka saci kayan abinci.
Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa zauna-gari-banzan sun kuma far wa wata babbar mota da aka laftawa kayan abinci dangin hatsi waɗanda aka yi niyyar rabawa a Birnin Kebbi.
Ta ce wawar kayan abinci a gidajen ajiyar kaya irin na Birnin Kebbi, ta faru a Abuja da garin Suleja a cikin jihar Neja.
Hakan na faruwa ne yayin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa wanda galibi aka yi imani ya faru ne sanadin cire tallafin man fetur da barin naira ta ƙwaci kanta a kasuwar canji.
Ta dai ambato Muhammadu Gwadangwaji, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar hatsi da ke Bayan Kara a Birnin Kebbi, wasu matasa sun ma cinna wuta kan shaguna da gidajen ajiyar kayan ‘yan kasuwa a lokacin wawason.
“(Jami’an tsaro) sun harba harsasai da hayaƙi mai sa hawaye sama, amma su (matasan) ba su razana ba. Sun kutsa kai suka shiga ciki, sannan suka washe gidan ajiyar kayan gwamnati da wasu shagunanmu na ‘yan kasuwa”.
Da yake mayar da martani, Ahmed Idris, wanda shi ne babban sakataren yaɗa labarai ga Gwamna Nasir Idris, cewa ya yi lamarin “abin takaici ne”.