Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da waɗansu kungiyoyin fararen hula sun yi tir da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da tsarin wuta mai daraja ta ɗaya wato Band A.
A zantawarmu da wasu daga cikin ’yan rajin kawo canji da kuma ’ya’yan kungiyar NLC, sun ce duk dalilan da jami’an gwamnati suka bayar kan karin kudin ba hujjoji ba ne.
A cewarsu, ko a ƙasashen da aka ci gaba, ana tallafa wa wasu ɓangarori kamar man fetur da wutar lantarki.
A jiya Laraba ce dai Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da ƙarin kuɗin kilowatt na wuta daga Naira 68 zuwa N225.
Wannan karin ga masu amfani da tsarin Band A da ke samu wuta na tsawon sa’o’i 20 a kullum za su riƙa biyan N135,000 kowane wata.
A taron da mataimakin shugaban NERC, Musiliu Oseni ya yi da manema labarai a Abuja, ya ce karin zai shafi kaso 15 na masu amfani da wutar lantarki miliyan 12 a Najeriya.
Shugaban yada labarai a hedikwatar NLC, Benson Upah, ya ce Ƙungiyar ta su za ta ɗauki matsaya kan mummunan ta’asar da aka yi na ƙarin kuɗin wuta.
Benson ya ce, za su sanar da matsayarsu idan masu ruwa da tsaki a kungiyar sun zauna.
“Shawarar da gwamnati ta yanke ba iya rashin tausayi ba ne, shawarace mai muni ƙwarai da gaske.”
Ya ce “wannan hukunci zai ƙara wa ’yan Najeriya wahalar da suke ciki. Sannan kuma zai ƙara gigita harkokin kasuwanci a ƙasar nan.
“Abin da in aka yi wasa zai kore masu saka hannun jari daga ƙasashen ƙetare a Najeriya.
Ya kara da cewa, “Mutanen da za su ci riba daga wannan tashin hankali da jama’a za su shiga su ne Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF.
“Abin tausayi! Za mu dawo gare ku a kan wannan batun nan gaba kaɗan, bayan masu ruwa da tsaki a kan wannan mataki na ƙungiyarmu sun zauna.”