Gwamnatin Nijar ta rusa majalisun kananan hukumomin kasar

0
148

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta rusa dukan majalisun kananan hukumomi na jiha da manyan birane a fadin kasar tare da maye gurbinsu da kantomomi.

A wata sanarwa da shugaban mulkin sojan kasar ya rattabawa hannu da aka karanta da gidan talbijin na kasar ya bayyana cewa an dauki matakin ne bisa kokarin wasu gyare-gyare.

Wadanda aka korar dai yawancinsu zababbu ne a tsohuwar gwamnati da suka share watanni 8 suna jan zarensu, tun bayan hanasu taba kudaden da’irorinsu a makon jiya akayi hasashen korarsu daga mukaman.

Tun a baya dai ‘Yan kungiyoyin fararen hula sun yi ta caccakar sojojin da cewa sun yi juyin mulki amma sun bar magajan gari kan mukamansu abin da ga al’ada ba a taba gani ba.

A ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 ne sojojin suka kifar da gwamnatin dimokaradiyyar kasar, karkashin jagorancin shugaba Bazoum Muhammane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here