Gwamnatin Nijar ta dage kan ficewar sojojin Amurka 

0
209

Hukumomin mulkin Nijar sun sake jaddada buƙatarsu na ganin cewa sojojin Amurka sun janye, lamarin da ke kawo cikas ga muradun tsaron Washington a yankin Sahel. 

A watan da ya gabata, shugaban mulkin sojan ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ya umarci sojojin Amurka da su fice bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar soji. 

Aƙalla jami’an sojin Amurka 650 ne ke jibge a Nijar domin sa ido kan ayyukan masu iƙirarin jihadi. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin Nijar ta ce ba su ci gajiyar yarjejeniyar da suka ƙulla da sojojin Amurka ba, don lamarin ya kasance ‘sakiyar da babu ruwa’. 

Ta zargi Amurka da cin zarafin Nijar tare da yin katsalandan a harkokin cikin gidanta da kuma neman taka rawa a alaƙar ƙasashen waje.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon sun yi watsi da kin amincewar da Nijar ta yi na yarjejeniyar sojin, suna masu cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu. 

Da farko dai gwamnatin mulkin sojan Nijar tana da zamantakewa mai kyau da Amurka, amma ta koma Rasha bayan yanke hulda da Faransa a bara.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here