Ambaliyar ruwa ya tafi da gidaje da dama a Kwara

0
133

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tafi da gidaje aƙalla 35 a yankin al’ummar Igbonna da ke karamar hukumar Oyun a jihar Kwara a ranar Alhamis.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da sama da mutane 1,000 suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama da aka yi a unguwar Iyara, hedikwatar karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin a ranar Juma’a, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Adekunle ya bayyana cewa ruwan saman ya ɗaiɗaita mutane da dama wanda ya sa kuma suka rasa matsugunansu. 

Ya ce “Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin Ogbonna da ke karamar hukumar Oyun ya yi mummunar illa ga al’umma. Abin ya shafi gidaje 35.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here