Gobara ta kone shaguna a kasuwar Yola

0
188

Wata gobara ta tashi a kasuwar garin Yola da ke karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, tare da ƙona shaguna da dama. 

Gobarar da ta afku ranar Litinin, ta kuma janyo wa ƴan kasuwa yin asarar kayayyakinsu.

Wani ɗan kasuwa mai suna Ali Kachalla wanda shi ne shugaban ƴan kasuwan na garin Yola, ya shaida wa BBC cewa ɓarnar da gobarar ta yi ba zai misaltu ba. 

Ya ce ta ƙona kusan kashi 80 cikin ɗari na kasuwar. 

“Gobarar ta ƙona kayayyaki da suka kai dubban miliyoyi. Da farko mun ɗauka wuta ce ta janyo gobarar, amma bayan washegarin yau mun gano cewa har da iska da tsawa a cikin abin da suka haddasa ta,” in ji shi. 

Kachalla ya ce mutane daga ko’ina ne suka kawo musu ɗauki. 

Ya kuma ce jami’an kashe gobara sun makara wajen kai ɗauki, saboda lokacin da suka iso wutar ta gama yin ɓarna. 

Ya ce mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta ta ziyarci kasuwar da safiyar Litinin domin jajanta musu, inda ta kuma ce gwamnati za ta yi binciki domin gano musabbabin tashin gobarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here