Bata-gari sun lalata turakun wutar lantarkin Gombe, Yola da Jalingo 

0
164
wutar lantarki

An jefa al’ummomin garuruwan Gombe, Yola da kuma Jalingo cikin duhu bayan da wasu bata-gari suka lalata turakun wutar lantarki guda huɗu a kan hanyar Jos zuwa Gombe mai karfin mega watt 330. 

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, kamar yadda babbar manajan kamfanin rarraba lantarki ta kasa (TCN), Ndidi Mbah ta bayyana a ranar Talata.

Ta ce hakan ya janyo katsewar wutar lantarkin da tashoshin Gombe, Yola, da kuma Jalingo ke bayar wa. 

“Lalata turakun wutar ya kuma shafi yawan wutar lantarkin da kamfanonin rarraba wuta ke bayar wa a sassan Yola da Jos,” in ji Ndidi. 

Ta ce TCN na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an mayar da wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa.

‘Muna kuma yin ƙoƙari domin sake gyara turakun wutar lantarku guda huɗu da aka lalata,” in ji sanarwar da hukumar ta fitar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here