Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda da dama a Neja

0
142

Rundunar sojojin sama ta Nijeriya ta ce jiragen yaƙinta sun yi luguden wuta kan maɓoyar ƴan ta’adda a yankin Shiroro na Jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar inda suka kashe da dama daga cikinsu.

Mai magana da yawun rundunar Air Vice Marshal Edward Gabkwet ne ya bayyana samun wannan nasara a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin ƙasar.

“A ƙaramar hukumar Shiroro, an kai samame ne a maɓoyar gawurtaccen ɗan ta’adda, Mallam Umar da kwamandoji da dama a dajin Alawa. An kai samamen ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa ƴan ta’adda da dama suna taruwa a wasu ɗakunan jinka,” in ji sanarwar.

Air Vice Marshal Gabkwet ya ƙara da cewa bayanan da suka tattara sun tabbatar da cewa waɗannan ƴan ta’adda su ne suka kai hari kan sojojin Nijeriya da ke yankin Bassa tare da binne abubuwa masu fashewa a hanyar Pandogari zuwa Alawa da ke ƙaramar hukumar ta Shiroro.

Ya ce nan da nan rundunar sojojin saman Nijeriya ta tura jiragenta inda suka “kawar da ƴan ta’adda da dama tare da lalata maɓoyarsu” abin da ba zai ba su damar kai hare-hare kan dakarun soji da fararen-hula ba. 

Kazalika sanarwar ta ce sojojin Nijeriya sun kai hari a yankin Neja Delta inda suka lalata matatun mai da aka kafa ba bisa ƙa’ida ba a ƙauyukan Ke, Egbema, Akaso Krakama, Krikama.

“Waɗannan samame sun yi matuƙar rage ƙarfin ƴan ta’adda a arewa maso yamma da kuma ɓarayin man fetur a Neja Delta waɗanda suke barazana ga tsaron ƙasa da al’ummarta,” in ji Air Vice Marshal Gabkwet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here