Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakarunta sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin saman Æ™asar, Edward Gabkwet ya ce cikin jerin wasu hare-hare ta sama da dakarun rundonin Hadin Kai da Whirl Punch suka Æ™addamar a jihohin biyu ya samu narasar lalata wasu shirye-shiryen ‘yan bindigar.
Edward Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayu dakarun ƙasar sun kai hari a garin Chinene da ke yankin tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno.
Ya ce dakarun sojin Æ™asar sun ga ‘yan bindigar na wani taro da ake kyautata zaton tattaunawa suke yi a lokacin da jirgin sojin ya kai musu hari tare da kashe su.
“Haka kuma a garin sojojinmu sun hangi wasu motocin yaÆ™i bakwai da ake zaton na ‘yan bindigar ne a Æ™arÆ™ashin wata bishiya, nan take su ma aka kai musu hari tare da lalata su”, in ji sanarwar.
Sanarwar ta Æ™ara da cewa “bayanan da muka samu bayan hare-haren sun nuna cewa an samu nasara, domin kuwa hare-haren sun halaka ‘yan bindigar da damarsu tare da lalata kayayyakinsu.”
Haka kuma sojojin sun ce sun kuma samu nasarar kai hari a Æ™auyen Allawa da ke kusa da Shiroro a jihar Neja, inda aka kashe ‘yan bindiga masu yawa.
Gabkwet ya ce sojojin sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri kan Æ™aura da ‘yan bindigar ke yi zuwa Æ™auyen, lamarin da ya tilasta wa mazauna Æ™auyen da dama tururuwar ficewa daga yankin sakamakon fargabar da suke yi.