Tinubu zai kori wasu daga cikin ministocin sa

0
125
Tinubu
Tinubu

Akwai alamun cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, zai yiwa majalisar zartarwa ta tarayya kwaskwarima.

A yanzu haka shugaban kasar yana fuskantar matsin lamba daga jam’iyyar sa ta APC, akan ya kori wasu daga cikin ministocin sa da suka gaza yin kokarin daya dace.

Ku Karanta: Tinubu ya sauka birnin Beijing na kasar China

Idan za’a iya tunawa a shekarar data gabata shugaba Tinubu ya samar da wani sashin bayar da bayanai akan kula da kokarin ministocin wanda mai taimaka masa ta musamman a fannin tsare tsare Hadiza Bala Usman, ke jagoranta don saka idanu akan ministocin da Kuma sauran masu rike da mukamai a Gwamnatin tarayya.

A lokacin samar da sashin Tinubu ya sha alwashin korar duk wani minista ko mai taimaka masa da aka samu da gazawa wajen yin aikin daya dace.

Ko a makon daya wuce sai da shugaban ya sauke shugaban jami’an tsaron farin kaya DSS, tare da maye gurbin sa da wani shugaban.

Wata majiya daga fadar shugaban kasar a yau lahadi ta tabbatar wa da jaridar Punch, cewa tabbas za’a yiwa majalisar zartarwa ta tarayya kwaskwarima a nan gaba kadan.

Majiyar wadda ta nemi sakaya sunan ta tace za’a cire wasu ministocin Sannan za’a canjawa wasu ma’aikatu don kara inganta aikin su.

Haka zalika wata majiyar ta ce tabbas shugaban kasar yana bukatar jajirtattun yan majalisar zartarwa da zasu taimaka masa wajen cimma manufar wasu tsare tsaren Gwamnatin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here