Jami’an tsaron farin kaya DSS sun kama shugaban kungiyar kwadago na kasa Joe Ajaero.
Wasu bayanan da aka samu daga bangaren jami’an tsaro sun tabbatar da cewa a yanzu haka Joe Ajaero, yana amsa tuhume-tuhume a hannun DSS.
Ku Karanta: Akwai rashin tausayi a karin kudin wutar lantarki da gwamnati ta yi – NLC
An kama Ajaero, a safiyar yau litinin sannan yana hannun DSS a babban ofishin hukumar dake birnin tarayya Abuja.
Tun kafin yanzu jami’an tsaro suka gayyaci Ajaero, bisa zargin an hada kai dashi a wasu ayyukan ta’addanci da sauran su.