ASUU ta bawa gwamnati wa’adin kwanaki 14

0
23

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 wajen shawo kan matsalolin dake tsakanin su, ko kuma kungiyar ta dauki mataki na gaba.

Bayar da wa’adin yazo a daidai lokacin da wa’adin farko da Kungiyar ta bayar na kwanaki 21 ya kare ba tare da gwamnatin ta saurari bukatar malaman ba.

Karanta karin wasu labaran:Dokar lamunin dalibai za ta hana da dalibai da yawa damar yin karatu – ASUU

Bukatun da ASUU ke neman gwamnatin tarayya ta biya mata sun hadar da cika alkawuran dake tsakanin su, musamman yarjejeniyar da akayi tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU a shekarar 2009, da shekarar 2021, sai batun biyan albashin malaman jami’o’i na wata 8 da ba’a biya su ba sakamakon yajin aikin da suka yi a shekarar 2022.

Shugaban kungiyar Emmanuel Osodeke, ya nuna takaici akan yadda gwamnatin tarayya take nuna rashin kulawa akan malaman jami’o’in da kuma jan kafa wajen aiwatar da abubuwan da ya dace a gudanar, sannan yace hakan shine yake ta’azara koma bayan fannin jami’o’in kasar nan.

Cikin Sanarwar da Kungiyar ta fitar ASUU tace bayar da wa’adin na Wannan lokaci ya zama wajibi saboda wa’adin farko da suka bawa gwamnatin ya cika tun a ranar 23 ga watan da muke ciki, Kuma babu wani matakin da aka dauka don shawo kan kalubalen da malaman ke fuskanta.

Sannan ASUU tace kar a zarge ta ko a dora mata laifi akan duk wani kalubalen da jami’o’in kasar nan zasu fuskanta sakamakon cewa sun bawa bangaren gwamnati duk wata damar da zasu bayar akan gyara barakar rashin biya musu bukatar tasu.

Har ila yau ASUU tace tana nemawa yayan ta hakkin da aka rikewa malaman da suke tsarin koyarwa a jami’o’i biyu, da kuma malaman da suke koyarwar wucin gadi, wanda suka ce tsarin biyan albashin bai daya na IPPIS ya kawowa biyan ma’aikatan nakasu.

Sannan ASUU ta nemi a fitar da kudaden da za’a gyara jami’o’in kasar nan, da Kuma biyan su alawus alawus da aka saka a kasafin kudin shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here