Masu bautar kasa zasu fara karbar naira dubu 77 a kowanne wata

0
38

Gwamnatin tarayya ta amince a fara biyan masu yiwa kasa hidima naira dubu 77 a matsayin alawus din kowanne wata

Za’a fara biyan kudin tun daga watan Yulin Wannan shekara ta 2024.

Hukumar kula da masu hidimtawa kasa NYSC ce ta sanar da hakan da yammacin yau laraba a shafin ta na Facebook, inda hukumar tace gwamnatin tarayya ta karawa duk masu aikin hidimtawa kasa alawus zuwa naira dubu 77.

Karanta karin wasu labaran:‘Labarin tura ‘yan NYSC zuwa Nijar ba gaskiya ba ne’

Kuma an samu tabbacin hakan a cikin wata takardar data fito daga hukumar dake tsara albashin ma’aikata ta kasa wadda aka fitar a yau dauke da sanya hannun shugaban hukumar Ekoi Nta.

Karin alawus ya baya rasa nasaba da karin mafi karanci albashin ma’aikata daga naira dubu 30 zuwa dubu 73.

NYSC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here