Gwamnatin tarayya ta fara biyan mafi karanci albashi

0
48
Tinubu
Tinubu

Bayan shafe watanni 7 ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da Kungiyar kwadago akan mafi karancin albashi da aka amince da naira dubu 70, gwamnatin tarayyar ta fara biyan ma’aikatan ta sabon albashin daga jiya Alhamis.

Sannan an yiwa kowanne ma’aikaci karin albashin daidai da matakin aikin sa.

Haka ya nuna cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya su miliyan 1 da dubu dari 2 zasu karbi sabon albashin a watan Satumba.

Babban akanta na tarayya Dr Oluwatoyin Madein, shine ya saka hannu akan takardar fara biyan sabon albashin tare da bayar da umarnin biyan ma’aikata.

Bayanin hakan ya fito daga wasu takardun da jaridar Punch, ta samu kuma sun fito daga hukumar dake tsara albashin ma’aikata ta kasa.

Daraktan yada labarai na ofishin babban akanta na tarayya Bawa Mokwa, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda yace an fara biyan sabon albashin a jiya Alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here