Rundunar NSCDC zata kori jami’in ta mai alaka da yan ta’adda

0
32

Rundunar tsaron al’umma ta farin kaya NSCDC ta kasa reshen jahar Zamfara, ta sanar da shirin korar wani jami’in ta mai suna ASCII Maikano Sarkin-Tasha daga aiki, akan zargin sa da taimakawa yan fashin daji da muggan kwayoyi da makamai.

Kwamandan rundunar na Zamfara Sani Mustapha, ne ya sanar da hakan a ranar asabar, lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Gusau.

Karanta karin wasu labaran:EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa rundunar yan sandan Zamfara tayi holin masu laifi su 17 a ranar juma’ar data gabata cikin su har da Sarkin-Tasha.

Mustapha, yace NSCDC ta firgita matuka lokacin da taji ance jami’in ta yana ma’amala da yan fashin daji, sannan yana yi musu safarar miyagun kwayoyi da makamai

Binciken farko da akayi ya nuna cewa an kama Sarkin-Tasha a wajen binciken ababen hawa dake hanyar Damba zuwa Sabon gida wanda hanyar take a karamar hukumar Gusau.

A lokacin ne aka same shi da wasu kwayoyi da kayan maye.

Sauran abubuwan da aka samu a wajen sa sun hadar da kwanson harsashi guda uku da wata na’ura mai hana babbar bindiga yin tasiri.

Shima babban kwamandan rundunar tsaron al’umma ta farin kaya NSCDC, na kasa Dr Ahmed Audi, ya shiga damuwa lokacin da aka bashi labarin cewa jami’in dake karkashin sa yana taimakawa yan fashin daji, kuma yayi ala wadai da yin hakan, inda yace Wannan aikin rashin sanin ya kamata ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here