Jami’an Yan sanda sun kama tsohon mai ajiyar kudi na masarautar Mutum biyu dake karamar hukumar Gassol a jihar Taraba mai suna Yahaya, bisa zargin sa da hannu a kisan da aka yiwa iyalan sarkin masarautar Mutum biyu Mai shari’a Sani Sulaiman, su bakwai bayan anyi garkuwa da su a watan Fabrairun shekarar 2023.
Kisan ya hadar da matan Sarkin su biyu da yayan sa biyar.
Rahotanni sun sun bayyana cewa an kama Yahaya bayan an daure wasu da ake zargin sune suka kashe iyalan Sarkin a Abuja inda suka ce tsohon mai ajiyar kudin na masarautar Mutum biyu shine yake kai musu bindiga kirar AK-47.
Wasu majiyoyi sun ce a yanzu haka ana cigaba da bincikar sa a shalkwatar yan sandan jihar Taraba dake Jalingo.
Wasu faifan bidiyon da aka rika yadawa sun nuna Yahaya yana tabbatar da cewa yana da hannu a kisan da aka yiwa iyalan sarkin masarautar Mutum biyu.
Yace wani mai suna Gambo Jimeta ne ya shirya zuwan masu garkuwar zuwa inda aka yi garkuwa da iyalan sarkin, sannan shine ya basu bindigar da yan ta’addan suke amfani da ita.
Sannan Yahaya, ya tabbatar da cewa an karbo bindigun ne saboda ayi garkuwa da mutanen.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Taraba, Kwache Gambo, yace zasu cigaba da samun bayanai daga wanda ake zargin.
Tun a baya masarautar Mutum biyu ta kori wanda ake zargin tsawon shekaru.