Yan Nigeria suna samun lantarki tsawon awanni 20 kowacce rana

0
83

Gwamnatin tarayyar Nigeria tace a yanzu haka kaso 40 na yawan al’ummar kasar suna samun wutar lantarki ta tsawon awanni 20 kowacce rana.

Ministan lantarki Adebayo Adelabu, ne ya tabbatar da hakan, da sanyin safiyar lahadi, lokacin da yake jawabi akan irin cigaban da ma’aikatar sa ta samun tsawon shekara guda, cikin wani bangare na shirye shiryen bukukuwan cikar Nigeria shekaru 64 da samun yancin kai.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin tarayya zata zubawa fannin lantarki dala miliyan 800

Adelabu, a cikin sanarwar da ya fitar yace ba haka Kawai ma’aikatar sa ta samu Wannan nasara ba, an samu hakan ne saboda jajircewar shugaban kasa Tinubu da ya taimakawa ma’aikatar.

Daga cikin manyan nasarorin da yace ya samu a ma’aikatar lantarki ta kasa shine samar da wuta mai karfin Megawatt 5,500, Kuma haka ne yasa mutane ke samun wutar awanni 20, kowacce rana.

A cewar Adelabu, za’a fahimci samun ingantuwar fannin lantarki in aka kwatanta da Lokacin baya, Kuma har yanzu yace suna kokarin sake inganta fannin.

Gwamnatin tarayya tace dole a tabbatar da wadatuwar karfin lantarki saboda habbaka tattalin arziki da cigaban masana’antu, saboda a haka ne kasashe irin su Korea, China, Turai, da Amurka suka samu cigaban kowanne fannin rayuwa.

MA’AIKATAR LANTARKI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here