Yan sanda sun kama masu shirya zanga zanga a jihar Kano

0
90

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama mutane 5 daga cikin masu shirya zanga zangar ranar 1 ga watan Octoba.

Daga cikin wadanda aka kama akwai jagoran zanga zangar ta (NPFM) na kasa Kwamared Abdulmajid Yakubu Dauda, da karin mutane 4.

Sauran mutanen sune Barista Yusha’u Sani Yankuzo, da Barista, Amina Bello, Kwamared Sani NaRago, sai Kwamared Anas Abdullahi.

Sakamakon shirin gudanar da zanga zangar tuni wasu daga cikin masu Sana’a a manyan tituna suka rufe shagunan su, don kaucewa afkuwar irin abinda ya faru lokacin zanga zangar watan Ogusta inda aka fasa shaguna da guraren gwamnati aka kwashe kayayyakin wajen.

Jaridar DAILYNEWS24, ta yi duba akan akan yadda wasu yan kasuwa suka rufe shagunan su a kasuwannin Rimi da Yan kura.

Wata majya ta ce tana zargin an  tafi da wadanda aka kama din zuwa Abuja, bisa hujjar cewa sun ki amsa gayyatar da yan sanda suka yi musu na zuwa a tattauna da su kafin shiga zanga zangar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here