Masu zanga zanga sun hadu da fushin jami’an tsaron Abuja

0
38

Masu zanga zangar da suka taru a kasuwar Utako, dake birnin tarayya Abuja sun gamu da fushin jami’an yan sanda.

Yan sandan sun tarwatsa su tare da harba musu hayaki mai sanya hawaye.

Karanta karin wasu labaran:Yan sanda sun kama masu shirya zanga zanga a jihar Kano

Tun da farko masu zanga zangar sun shirya taruwa a kasuwar Utako mai dauke da mutane masu yawa dake zuwa cikin ta yin kasuwanci.

Da sanyin safiyar yau Talata ne mutanen suka aiwatar da aniyar su ta gabatar da zanga zangar don nuna fushin su akan tsadar rayuwa da neman dawo da tallafin man fetur.

Wannan zanga zangar tayi kama da wadda aka taba yi a watan Ogustan shekarar da muke ciki, inda aka shirya waccan zanga zangar don neman samun shugabanci na gari.

A Wannan lokaci kuwa batun tsadar rayuwa, tashin farashin kayan masarufi, da kuncin rayuwa sune dalilan masu shirya zanga zangar.

Wakilin jaridar Daily Trust, ya bayar da labarin yanda jami’an sojoji suka yi cincirindo a babbar hanyar Kubwa zuwa Zuba, dauke da manyan kayan aiki.

A makamancin Wannan labari, a jihar Legas ma an samu wadanda suka fita zanga zangar ta yau Talata.

Duk da cewa jami’an tsaro sun ja kunnen mutane akan kaucewa zanga zanga amma hakan bai hana wasu fitowa ba.

A Wannan lokaci dai zanga zangar bata samu armashi ba in aka kwatanta da ta watan Ogusta, sakamakon cewa ba’a samu fitowar mutane da yawa ba, kuma ba a kowacce jiha aka fito ba, sai Abuja da Legas da kuma wasu guraren yan kalilan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here