Yan Boko Haram sun yanka manoma a jihar Borno

0
61

Awanni kadan bayan shugaban kasa Tinubu, da Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, sun bawa manoma tabbacin cewa gwamnati zata kare rayukan su, an samu wasu mayakan boko haram sun yiwa manoma 5 yankan rago a garin Ngoshe, dake karamar hukumar Gwoza.

Tinubu da Zulum, a jawabin da suka gabatar jiya Talata yayin bikin cika shekaru 64 da samun yancin kai da Nigeria tayi, sun ce manoma zasu samu tsaro ta yanda basu da fargabar zuwa gona don samar wa Nigeria abincin da ake bukata.

Karanta karin wasu labaran:‘Yan Boko Haram 78 sun mika wuya ga hukumar soji a Borno

Shi kuwa Tinubu cewa yayi gwamnatin sa ta samu nasara akan Boko Haram tare da kashe manyan mayakan ta.

Masu majiyoyi sun ce manoman a baya anyi garkuwa da su, sannan aka kashe su, inda mayakan suka kashe wani dan kungiyar tsaron sa kai ta CJTF, mai suna Jubril Zarana, wanda yake aikin samar da tsaro tare da jami’an tsaro.

Wata majiya mai tushe daga Gwoza ta bayyana damuwar ta akan garkuwar da akayi da manoman su 15 wanda suka kunshi maza, mata, da kananun yara, kuma daga cikin wadannan mutane ne aka kashe biyar.

Mayakan sun yiwa manoman kwantan bauna lokacin da suka shagala da aiki a gonakin su.

Ance jami’an tsaro da yan sa kai sun yi iya bakin kokari wajen ceto mutanen da aka sace amma burin su bai cika ba, an kashe jami’in sa kai Jubril Zarana, lokacin da yake kokarin tsare rayuwar mutane.

Manoman da boko haram ta yanka bayan yin garkuwa da su sun hadar da Isa Musa Moh’d Diyara, Doglas, Salawuddin Suleman Dauda Lawan, Maryam Gwambran, Matan Kaka Mobil Aga da Baba Amos.

Bayan kashe mutane biyar sun Kuma saki mata uku, tare da rike sauran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here