Jihohi zasu fara siyar da shinkafa mai tallafin gwamnati

0
22

Gwamnatin tarayya ta fadada shirin siyar da shinkafa a farashi mai sauki zuwa jihohi baki daya inda za’a kaddamar da shirin a Kano Lagos da Borno.

Daya daga cikin jagororin ma’aikatar noma ta kasa ne ya sanar da hakan a ranar litinin data gabata.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnati ta fara siyar da buhun shinkafa akan naira dubu 40

A farkon watan Satumba ne ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari, ya kaddamar da shirin siyar da shinkafar ta gwamnati a birnin tarayya Abuja, inda za’a siyar da shinkafar mai nauyin kilogram 50 akan naira dubu 40, sannan yace shirin zai kawo sauki akan halin yunwa da Nigeria ke ciki.

A cewar gwamnatin tarayya siyar da shinkafar akan farashin naira dubu 40 zai ragewa yan kasa radadin hauhawar farashin kayan masarufi da suke tashi babu kakkautawa a kasuwanni.

A halin yanzu dai farashin buhun shinkafa a kasuwanni yakai naira dubu 90 zuwa 100, akan kowanne buhu mai nauyin kilogram 50.

Gwamnatin tarayya ta ce tana fitar da Tan dubu 30 na shinkafar akan farashin gwamnati.

Kamar yadda ma’aikatar noman ta sanar daga yanzu zuwa kowanne lokaci zasu kaddamar da shirin siyar da shinkafar a jihohin Kano, Lagos, da Borno.

Lokacin da aka yi tsokacin cewa wasu mutane sun dakile shirin siyar da shinkafar ga talakawa a Abuja, ma’aikatar noman ta musanta zargin.

MA’AIKATAR NOMA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here