Cikin kwana 30 ICPC ta kwato biliyan 13 da aka sace

0
74

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da dangogin su ta kasa ICPC, ta samu nasarar kwato naira biliyan 13, cikin kwanaki 30, bayan an karkatar da kudaden zuwa wata hanya da bata dace ba.

Hukumar tace Wannan yana daga cikin manyan nasarorin da ta taba samu a karamin lokaci.

Karanta karin wasu labaran:EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku

ICPC ta kara da cewa kwato kudin na daga cikin tsare tsare da take yi na kakkabe cin hanci daga yanzu zuwa shekarar 2028.

Hukumar tace zata fadada kokarin ta a fannin aiwatar da al’amuran kudi a bayyane da samun hadin kan masu ruwa da tsaki.

Shugaban hukumar ICPC Dr. Musa Adamu Aliyu, ne ya sanar da hakan a birnin tarayya Abuja lokacin da yake bayyana sabon shirin hukumar na ganin karshen ayyukan cin hanci daga yanzu zuwa shekarar 2028.

Ya kuma zayyano wasu daga cikin nasarorin da hukumar ta samu da suka hadar da yin amfani da fasahar sadarwa a yaki da cin hanci.

ICPC tace ba aikin yaki da cin hanci da rashawa har akai ga samun nasara ba na hukuma daya bane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here