ASUU zata shiga yakin aiki sai baba ta gani

0
81

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU tace zata shiga yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawuran data daukar wa kungiyar tun a shekarar 2009.

Shugaban kungiyar ASUU shiyyar Bauchi, Farfesa Timothy Namo, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da yake jawabi ga wani taron manema labarai a Jos.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin tarayya zata hana kungiyar ASUU shiga yajin aiki

Yace kungiyar ta gudanar da taruka a baya tare da bawa gwamnati wa’adin kwanaki don magance kalubalen da ke tsakanin ASUU da gwamnatin, amma har yanzu babu wani kwakkwaran matakin da bangaren gwamnatin ya dauka.

Namo, ya kuma ce babu daya daga cikin yarjejeniyar da gwamnati ta aiwatar.

Yace yan Nigeria su dorawa gwamnati alhaki in har kungiyar ASUU ta rufe jami’o’in kasar nan.

Daga cikin bukatun ASUU akwai neman biyan su albashin da gwamnati bata biya yan kungiyar ba na tsawon watanni 8 lokacin da Kungiyar ta shiga yajin aiki, sai biyan su alawus da suke bi, tare da sakin kudaden gyaran jami’o’in da aka saka cikin kasafin kudin shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here