Jam’iyyar APC ta sake shigar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC kara gaban wata Kotun tarayya dake birnin Kano.
Jam’iyyar ta shigar da sabuwar karar ce a yau juma’a, inda take neman kotu ta haramtawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC bayar da katin zabe ga wadanda zasu yi zaben kananun hukumomin a cikin Wannan wata.
Karanta karin wasu labaran:Kotu ta hana jam’iyyu 19 kawo wa KANSIEC matsala a zaben kananun hukumomin KanoÂ
Jam’iyyar APC da shugaban ta na Kano Abdullahi Abbas, sun shigar da karar ta hannun wani mai suna Ismail Abdulaziz.
Sannan sun nemi a hana hukumar zabe ta Kano, KANSIEC cigaba da shirin gudanar da zaben a ranar 26 ga watan Oktoba.
Wadanda aka shigar karar sun hadar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, da hukumar INEC, sai kwamishinan shari’a na Kano, da ministan shari’a na kasa.
Har ila yau, masu shigar da karar sun ce suna so a fayyace musu cewa ko hukumar zaben tana da hurumin karbar kudin shiga na naira miliyan 9 da miliyan 4, daga wajen masu son shiga takarar shugabancin kananun hukumoni da Kansiloli.
Bayan gabatar da karar kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Oktoba don bawa masu karar da wadanda suke kare kansu damar shirya bayanan da za’a yi amfani da su don cigaba da yin shari’ar.