An fara zaben kananun hukumomin Rivers babu yan sanda

0
65

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Rivers RSIEC, ta fara aiwatar da zaben kananun hukumomin jihar duk da cewa zaben ya gamu da kalubale da dama kafin yau.

Tuni aka kammala rarraba kayan aikin zaben a daukacin kananun hukumomin jihar Rivers har ma ana cigaba da kada kuri’a.

Gwamnan jihar Siminalayi Fubara, dama ya sha alwashin gudanar da zaben duk rintsi.

Karanta karin wasu labaran:Rikici ya kunno tsakanin gwamnan Rivers da shugaban yan sandan kasa

A shekaran jiya ne rundunar yan sandan jihar tace jami’an ta ba zasu je wajen zaben ba, don yin biyayya ga umarnin wata babbar kotun tarayya data ce kar jami’an su halarci gurin zaben kananun hukumomin jihar Rivers.

Sai dai gwamnan jihar Siminalayi Fubara, yace shugaban yan sandan kasa shine mai alhakin duk wani abun daya faru mara dadi a Rivers.

Kafin fara zaben a yau an samu fashewar wasu abubuwa a sakatariyar jam’iyyar APC reshen jahar ta Rivers, hakan kuma ya lalata bangarori da dama na babban ofishin jam’iyyar.

Suma wasu magoya bayan ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, sun gudanar da zanga zangar kin jinin gudanar da zaben a yau asabar.

Dama tun kafin yanzu ana ganin rikicin siyasar dake tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara, da tsohon mai gidan sa Wike, shine ya dagula al’amuran jihar Rivers da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here