Gwamnatin Zamfara ta biya tsaffin ma’aikata naira biliyan 9

0
25

Gwamnatin Zamfara ta biya tsaffin ma’aikatan jihar kudin sallamar ma’aikaci da yawan su ya kai naira biliyan 9, da gwamnatin jihar ta gaza biya tun a shekarar 2011.

Gwamnan jihar Dauda Lawal, ne ya bayar da umarnin biyan ma’aikatan, wanda aka fara tun a watan Fabrairun shekarar da muke ciki.

Wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Idris, ya fitar a yau asabar tace, an biya kudaden da yawan su yakai naira biliyan 4 da miliyan dari 5, a rukuni 9 da aka yi ana biyan kudaden.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Zamfara ta musanta ciyo bashin naira biliyan 14.26

Sannan yace an biya tsaffin ma’aikatan kananun hukumomi kudin sallamar su daga aiki da yakai naira biliyan 4 da rabi.

Yace a cikin tsaffin ma’aikatan 3,880 da aka tantance 2,666 sun karbi hakkin su, da tsohuwar gwamnatin jihar ta gaza biya.

Ma’aikatan da suka kammala aiki a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2024 ne aka biya kudin.

Tun a watan Fabrairu ne gwamna Dauda Lawal, ya kafa kwamitin tantancewa da biyan tsaffin ma’aikatan hakkin su, bayan da ya hau mulkin jihar tare da samun tarin bashin albashin da ma’aikata ke bin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here