Shugaba Tinubu yace bai damu da yin mulki a karo na biyu ba

0
135

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya jaddada aniyar sa ta sauya fasalin kasar nan da kuma kirkirar hanyoyin samun arziki ga Nigeria.

Shugaban wanda ya bayyana hakan a ranar asabar yace zaben shekarar 2027, ba shine abinda ya mayar da hankali ba a yanzu, sai dai yana nemar wa kasar yanda zata dogara da kanta a nan gaba.

Karanta karin wasu labaran:Shugaban kasa Tinubu zai shafe makonni 2 yana hutawa a Burtaniya

Ya sanar da hakan lokacin daya halarci babban taron jam’iyyar APC shiyyar kudu maso kudu da akayi a jihar Legas.

Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso kudu, kuma gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ne ya kasance mai masaukin baki a wajen taron.

Tinubu, ya bayyana hakan ta bakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, wanda shine ya wakilce shi a wajen taron, kuma a cewar sa shugaban ya damu da irin halin kuncin rayuwa da yan Nigeria ke ciki, sannan yace nan gaba komai zai daidaita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here