Majalisar dattawa ta shiga ganawar gaggawa akan yancin kananun hukumomi

0
58

Yan majalisar dattawa sun yi wata ganawar gaggawa akan tabbatar da an aiwatar da hukuncin Kotun koli akan yancin kananun hukumomin kasar nan 774.

Sanata Tony Nwoye, na jam’iyyar LP daga jihar Anambra, shine ya dauko batun kananun hukumomin a zaman majalisar na yau laraba.

Yayi zargin cewa wasu gwamnonin suna kokarin bijirewa umarnin kotun koli akan yancin kananun hukumomin ta hanyar samar da wasu dokokin da suka sabawa hukuncin kotun kolin daga majalisun dokokin jiha.

Karanta karin wasu labaran:Majalisar wakilai ta hana a bawa Maiduguri tallafin kudi

Yace gwamnonin suna kirkirar dokokin da zasu tilastawa shugabannin kananun hukumomi tura kudaden da gwamnatin tarayya ta basu zuwa asusun hadakar gwamnatin jiha da kananun hukumomi, wanda kotun koli ta ayyana shi da bai halasta ba.

Sai dai Sanata Adamu Aleiro, ya bukaci a dakatar da mahawara akan batun inda yace dole ne ayi biyayya ga umarnin kotun koli akan yancin kananun hukumomin, haka aka yi kuwa inda shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya amince da maganar tasa.

SENATE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here