Majalisar kasa tana son samar da jami’a mai sunan shugaba Tinubu

0
17

Akwai yiwuwar samun sabuwar jami’a a kasar nan, biyo bayan yin karatu na farko akan kudirin samar da jami’ar tarayya da za’a rika koyar da Ilimin mabanbantan yare ko harshe wato (languages) a turance, mai sunan shugaban kasar nan Bola Ahmad Tinubu.

Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu, ne ya gabatar da kudirin samar da jami’ar, wanda ya samu goyon bayan yan majalisa 8, da suka ce hakan zai kara daga darajar koyar da ilimi a kasar nan.

Karanta karin wasu labaran:Majalisar dattawa ta shiga ganawar gaggawa akan yancin kananun hukumomi

Kudirin samar da jami’ar yace za’a yi amfani da ita wajen farfado da harsunan Nigeria, da al’adun ta, ba tare da nuna bangaranci ko banbanci ba.

Daga cikin abubuwan da za’a rika yi a jami’ar akwai Diploma, digirin farko, dana biyu, sai kuma sauran binciken da za’a rika yi a Makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here