Gwamnatin Kano ta musanta zargin fito da Sheikh Abduljabbar daga gidan gyaran hali

0
64

Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin da wasu ke yi na cewa tun kafin yanzu tana da manufar fito da Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara, daga gidan gyaran hali.

Kwamishinan harkokin addini na Jihar Kano Sheikh Tijjani Sani Awwal, shine ya musanta zargin lokacin da yake ganawa da tashar Radiyon Premier, dake jihar Kano.

Kwamishinan yace gwamnatin Kano, tana mutunta bangaren addini da shari’a, sakamakon cewa Wannan magana an kammala ta, Kuma gwamnatin bata shiga cikin sha’anin shari’a.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda sun fara mallakar gidaje a jihar Kano

Idan za’a iya tunawa dai tsohuwar gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje, ce ta gurfanar da Sheikh Abduljabbar, bisa zargin sa da yin amfani da wajen karatun sa, wajen cin zarafin Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

A lokacin kammala shari’ar kotu ta samu Malamin da laifin cin zarafin Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW, a wasu daga cikin karatuttukan sa, tare da yanke masa hukuncin kisa.

An yanke masa hukuncin ne a ranar 15 ga watan Disamba na shekarar 2022.

Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara, ya daukaka kara zuwa kotu ta gaba, sai dai har yanzu ba’a bayyana lokacin fara sauraron karar ba.

Masu zargin gwamnatin Kano da yunkurin fito da Malamin daga gidan yari, sun ce gwamnatin zata yi hakan ne don samun goyon bayan daliban sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here