Kotu ta saka lokacin cigaba da shari’ar masarautar Kano

0
61

Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta sanya ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba domin cigaba da sauraron karar da aka shigar kan rikicin masarautar Kano.

A ranar litinin ne alkalan Kotun uku karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Mustapha,  suka jingine yin hukunci a kararrakin da aka shigar mata.

Kararrakin da ke gaban kotun daukaka karar su ne na Alhaji Aminu Ado Bayero da babban lauyan jihar Kano da kuma wasu mutum 10 da ke da lambar daukaka kara CA/KN/166/M/2014 da kuma mai lamba CA/KN/126/M/2024 kan nadin sarkin, tsakanin majalisar dokokin jihar Kano da Alhaji Aminu Babba Dan Agundi da Kuma karin wasu mutane shida.

Karanta karin wasu labaran:Jam’iyyar NNPP zata ladabtar da gwamnan jihar Kano 

Akwai kuma kudirin dakatar da aiwatar da hukuncin Kotu na ranar 25 ga watan Yuli.

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano karkashin Mai shari’a Abdullahi Liman ta soke matakin da Gwamna Abba Yusuf ya dauka na tsige Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero tare da nada Muhammadu Sanusi II a ranar 23 ga watan Mayu.

Kotun ta kuma yi watsi da dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartar a shekarar 2024 kan masarautun, kotun ta ayyana gyaran da aka yiwa dokar nada sarakunan Kano a matsayin wadda ba’a amincewa ba.

Bayan haka ne Kuma wata babbar kotun jihar Kano ta hana Ado Bayero ayyana da kansa a matsayin sarkin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here