Kwamishinan Jigawa ya karyata zargin lalata da matar aure.

0
30

Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman ta jihar Jigawa Auwal D. Sankara, yace wasu rahotanni da aka samu wasu kafafen yada labarai suka wallafa ya ja hankalin sa, inda ake zargin cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama shi bisa zargin lalata da wata matar aure

Ina so in bayyana cewa wadannan zarge-zargen gaba daya karya ne, Kuma marasa tushe, wanda aka yi da nufin bata min suna. Ina kira ga jama’a da su yi watsi da wannan kagaggen labari, wanda wasu ‘yan siyasa suka hada don lalata hali na da mutuncina, inji kwamishinan.

Karanta karin wasu labaran:Rundunar Hisbah ta dauki hanyar kawo karshen Caca a Kano

A matsayina na mai aure, ina matuÆ™ar mutunta tsarin aure kuma ba zan taÉ“a yin wani abu da ya saba darajar aure ba. Na tsaya tsayin daka don kiyaye dabi’u da ka’idodin da na tsaya a kai, inji Auwal D. Sankara.

Ina daukar wannan al’amari da muhimmanci kuma zan bi matakin shari’a a kan wadanda ke da alhakin yada wannan labarin na karya.

Auwal D. Sankara (FICA)

Kwamishinan ma’aikatar Ayyuka na Musamman Jihar Jigawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jaridar Daily News 24, ta samu da sanyin safiyar yau asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here