An Sace naira biliyan 2 da za’a rabawa marayun jihar Kebbi

0
23

Gwamnatin jihar Kebbi ta dauki matakin magance zargin satar kudi a asusun marayun jihar, kimanin naira biliyan 2 da miliyan dari 1 da kungiyar Musulmi ta duniya ta bayar don raba wa marayu 1,849 a jihar.

Lokacin wani taron manema labarai a Birnin Kebbi da Kwamishinan Harkokin Addinai, na jihar Alhaji Muhammad Sani Aliyu, ya gabatar, ya bayyana cewa Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya bayar da umarnin bincike tare da kwato kudaden cikin gaggawa. 

Kwamitin zai binciki yadda aka yi amfani da na’urar cirar kudade ta (POS) wajen kwashe kudin.

Kranta karin wasu labaran:Gwamnatin Kebbi zata hukunta daliban kwalejin kiwon lafiya ta Jega

Kwamishinan ya ce duk bankin da aka samu da hannu a wannan laifi za a dauki matakin daya kamata a kansa. 

Ya kuma mika godiya ga kungiyar musulmi ta duniya bisa wannan karamci da suka nuna, ya kuma bayyana cewa ofishin kungiyar da ke Kaduna ya yi alkawarin bayar da hadin kai wajen kwato kudaden.

Kwamitin karkashin jagorancin kwamishinan harkokin addinai ya kunshi wasu kwamishinoni biyu da masu ba da shawara na musamman da wasu manyan sakatarorin ma’aikatun jihar biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here