Isra’ila ta sake kaiwa Lebanon hari

0
15

Jiragen yakin Isra’ila sun Kuma kai hare hare zuwa kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon.

Harin shi ne karo na biyu da Isra’ila ke kaiwa tun bayan da wani jirgi mara matuki ya kai hari gidan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Asabar.

Karanta rin wasu labaran:Tawagar Hamas ta shiga tattaunawar tsagaita wuta kan yakin Gaza 

Zuwa yanzu dai Hezbollah ba ta dauki alhakin kai harin ba.

Natanyahu ya sha alwashin cewa Iran da wakilanta za su gane kuskuren su, kuma yan sa’o’i kalilan bayan haka Israila ta fara kai manyan hare haren zuwa Lebanon.

Har yanzu Isra’ila ba ta mayar da martani kan Iran ba, bayan harin makamai masu linzami da ta kai mata a farkon wannan watan.

Harin dai yayi matukar tasiri a kasar Isra’ila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here