Nigeria tana bawa Togo, Benin da Niger lantarki ta tsawon awanni 24

0
49

Babban daraktan gudanarwa na Hukumar rarraba wutar lantarki ta kasa TCN, Sule Abdulaziz ya ce kasashen Togo da Benin suna samun wutar lantarki ta sa’o’i 24 daga Najeriya.

Yace Nigeria tana bawa Kasashen Togo, Benin, da Niger wutar lantarki, sannan kasashen suna shafe awanni 24 ba tare da an dauke musu wuta ba.

Abdulaziz, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da gidan talbijin na channels a ranar lahadi.

Karanta karin wasu labaran:Turken wutar lantarkin Nigeria ya lalace karo na uku a mako daya

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa yan Najeriya da dama ba sa samun wutar kamar haka, cewa yayi yan Najeriya su na samun wuta sosai sai dai ba a ko’ina ba. 

Yace Wadanda suke shan wuta a karkashin tsarin Band A suna samun lantarki ta awa 20 zuwa 22 a kowacce rana.

Abdulaziz, ya tabbatar da cewa Nigeria zata fara samun isasshiyar wutar lantarki nan da shekaru biyar masu zuwa.

Inda yace ministan lantarki yana kokari domin tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa akwai banbanci tsakanin TCN da tsohuwar hukumar samar da lantarki ta NEPA, wanda ya bayyana cewa lokacin da ake karkashin Nepa, su ne suke samar da wutar, su kuma rarraba ta, tare da yin kasuwancinta, amma yanzu rarraba wutar kawai suke yi. 

Sannan ya kara da cewa idan aka samu tangarda daga babban layin lantarki na kasa, ana dora musu laifi saboda ana yi musu kallon matsayin da NEPA take a baya.

Yace Idan an samu tangardar wuta ba dole ne ta zama daga TCN ba, domin za a iya samuwa daga sauran bangarori.

Shugaban na TCN ya kuma bayyana lalacewar kayan aiki, a matsayin wata matsala da ke addabarsu, inda ya ce, yawancin kayayyakin aikin da suke amfani da su sun haura shekara 50 ana yin amfani da su ba’a canja ba.

A game da tsadar lantarki kuwa, Abdulaziz ya ce, wutar lantarki tana da sauki a Najeriya, idan aka kwatanta da wasu kasashen Afirka irin su Burkina Faso da Senegal da Jamhuriyar Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here