An kama mace mai shekaru 54 tana yin safarar makamai

0
37

Jami’an yan sanda sun kama wata mata mai shekeru 54 bisa zargin ta da yin safarar harsashi guda 350 a Jihar Yobe.

Rundunar ’yan sandan jihar na zargin matar da safarar makamai ba bisa ka’ida ba daga garin Buni Yadi zuwa Damaturu.

Karanta karin wasu labaran:Cutar amai da gudawa ta kashe mutane 9 a Jihar Yobe

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce an samu nasarar kama matar a Damaturu bayan samun bayanan sirri a kanta

An samu nasarar ce bayan an kama wata mota kirar Golf 3 sannan aka gudanar da bincike har aka gano harsasai guda 350 samfurin 7.62x39mm a boye cikin kayan wadda ake zargin.

Kakakin yan sandan yace a halin yanzu ana yi mata tambayoyi domin gano wadanda take kaiwa makaman.

Dungus ya bayyana cewa kwamishinan ’yan sanda na Jihar Yobe, Garba Ahmed, yana kan aniyarsa ta yaki da laifuka tare da kira ga jama’a su ci gaba da ba wa jami’an tsaro hadin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here