Daliban Zamfara sun shiga mawuyacin hali a kasar Cyprus

0
28

Wasu dalibai yan asalin jihar Zamfara masu karatu a bangare daban-daban a kasar Cyprus, sun koka akan yadda suka ce gwamnatin jihar ta manta da su ba tare da biyan kudaden karatun su ba.

Daliban sun shaidawa BBC cewa yanzu haka basu san matsayar karatun su ba, saboda makarantar su ta gaji da jiran a biya masu kudin karatu daga bangaren gwamnati har sun dakatar da su, lamarin da ya jefa da dama a cikin su cikin mawuyacin halin rayuwa.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda zasu kaiwa al’ummar Zamfara harin ramuwa

Daliban musamman mata, da wasun su suka shafe shekaru a kasar, sun bayyana halin talauci da rashin damar zuwa asibiti baya ga tsangwama da suke fuskanta, tsawon shekaru, abinda hakan ke barazanar jefa wasun su aikata ba daidai ba.

Sun ce yanzu haka suna fuskantar barazanar kora daga Cyprus saboda takardunsu na neman izinin tafiya sun lalace kuma babu halin yin wasu.

Daya daga cikin daliban ya shaidawa BBC cewa tun a lokacin tsohon gwamna, Bello Matawalle aka bude scholarship suka cike aka dauke su, aka kawo su karatu Cyprus su 93, wanda a yanzu sun dawo 88.

BBC ta tuntubi gwamnatin jihar Zamfara a kan wannan batu, inda Malam Sulaiman Bala Idris mai magana da yawun gwamnan jihar, ya ce su na sane da halin da daliban ke ciki, kuma matsala ce da suka gada, amma yanzu haka suna kokarin daukar matakan gaggawa domin taimakawa daliban.

Mai magana da yawun gwamnan ya kuma kara da cewa a cikin yan kwanakin nan, gwamnatin Zamfara za ta kai masu dauki, kuma za ta biya duk kudaden da ake bin daliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here