An kori yan jarida 14 daga fadar gwamnatin Kano 

0
27
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Kano ta dakatar da yan jarida 14 da ke aiki a fadar gwamnatin jihar daga aiki tare da neman sauyinsu daga hukumomin da suka turo su

A wani sako da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ga wadanda abin ya shafa, ya umarce su da su koma wuraren aikinsu, tare da neman hukumomin su su aika da wadanda zasu maye gurbinsu.

Karanta karin wasu labaran:Babbar mai shari’ar jihar Kano ta yiwa fursunoni afuwa

Sai dai babu wani dalili da kakakin ya bayyana na daukar matakin, amma ya bukaci su bi umarnin wanda ya fara aiki daga yau Talata.

Sakon da ya rubuta a shafin WhatsApp na tawagar ‘yan jaridar da ke aiki a fadar gwamnatin ta Kano, Sanusi ya bayyana cewa, abin takaici a lokacin da ya yi tafiya zuwa kasar Serbia a makon da ya gabata, wasu abubuwa sun faru, saboda haka akwai bukatar a dauki mataki.

Wasu daga cikin yan jaridar da abin ya shafa sun hada da na kafofin yada labarai na gwamnatin jiha da na tarayya da kuma masu zaman kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here