Yan ta’adda sun kakabawa al’ummar Katsina biyan harajin dole

0
72

Al’ummomin wasu garuruwa shida na karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina, sun ce suna cikin halin tsaka mai wuya, sakamakon harajin naira miliyan goma da yan bindiga suka ce se sun biya,  baya ga hare-haren da yan bindigar ke yawan kai wa garuruwan, suna sace mutane don neman kudin fansa tare da sace dabbobi da sauran dukiyoyi.

Wata majiya ta shaida wa BBC, cewa yanzu haka akwai mutum fiye da 20 da yan bindigar suka yi garkuwa da su, tare da neman biyan kudin fansa.

Karanta karin wasu labaran:Masarauci ya shiga hannu akan zargin ta’addanci a Katsina

Bayanan da BBC ta tattara sun ce yan bindigar suna hana jama’ar garuruwan sakewa har abin ya kai ga hana su zuwa gona.

Wani mutumin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana irin halin da suke ciki, na kunci da rashin kwanciyar hankali saboda yan ta’addan.

Yace da dare ba ka bacci, da rana ba ka zuwa gona, rayuwa na cikin matsala.

Yace a halin da suke ciki an yanka musu haraji, na miliyn 10, duk mai mata zai bada naira 21, 500.

Mutumin ya ce kusan kullum sai yan bindigar sun yi wani nau’in cin zarafi ga jama’a, ko a gonaki ko a gida.

Yayin da aka tuntubi Dakta Nasiru Mua’azu, kwamishinan tsaro na jihar ta Katsina, ya yi bayani cewa akwai wani lokaci da yan bindigar suka fafata da sojoji har ta kai ga sojojin sun fatattake su tare da kwace musu babura, inda yace yana zargin ramuwar gayya ce yan bindigar ke yi a kan jama’a.

Mu’azu ya ce gwamnati na yin bakin kokarin ta domin magance wannan matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here