Majalisar wakilai ta bayar da umarnin bincikar yawan lalacewar lantarki

0
42

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitin ta da ke kula da harkokin wutar lantarki ya gudanar da bincike kan matsalar yawan lalacewar babban layin samar da lantarki na kasa tare da bayar da rahoton cikin mako uku masu zuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, matakin ya biyo bayan amincewa da bukatar hakan da dan majalisa Mansur Mano Soro, daga jihar Bauchi ya gabatar a yau Laraba.

Karanta karin wasu labaran:Wutar lantarkin arewacin Nigeria ta sake lalacewa

Dan majalisar ya bayyana takaici kan matsalar lalacewar babban layin lantarkin na kasa dake faruwa kamar wasa a kwanakin nan, lamarin da ke jefa al’umma cikin rashin wuta da lalacewar sha’anin kasuwancin dake bukatar lantarki. 

Ya ce, wutar lantarki aba ce da ta zama dole wajen babbaka tattalin arziki da kuma cigaban kasa.

Mansur ya nuna takaicin sa kan yadda aka samu matsalar lalacewar babban layin wutar na sau takwas a cikin wannan shekara ta 2024.

Ya ce sakamakon matsalar lalacewar, gaba yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas sun kasance cikin duhu, da tsadar rayuwa.

Ya kuma ce abin takaici ne yadda matsalar ke faruwa a daidai lokacin da ministan wutar lantarkin ke ba wa ‘yan Najeriya tabbacin ingancin samar da wutar, abin da ya sa gwamnati ta ce ya zama dole a kara kudin wutar.

Yanzu dai an kara kudin lantarkin amma babu abinda hakan ya tsinana sai koma bayan da aka samu na rashin wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here