Mahukuntan tarayya Abuja sun tabbatar da kama wani babban dan kwangila daga kasar waje kan zargin sace fitilun kan titi.
Asiri dan kwangilar ya tonu bayan da farko an yi zargin cewa masu jari bola ne suke sace fitilun kan titin.
Karanta karin wasu labaran:Almajiran Abuja zasu dauki azumi saboda kamen da za’a fara yi musu gobe
Shugaban hukumar Kula da Birnin Abuja Felix Obuah, ne ya sanar da haka a yayin rangadin aikin gyaran fitilun kan titin da ministan birnin, Nyeson Wike ya ba da umarni.
Kawo yanzu Felix Obuah bai bayyana sunan da kasar wajen ko kamfaninsa ba, amma ya ce kamfanin sananne ne, kuma wanda ake zargin zai fuskanci hukunci.
Ya bayyana cewa dan kasar wajen da ke tsare shi a halin yanzu, yana sace fitilun titin da nufin a ba shi kwangilar sake sanya fitilun
Obuah ya ci gaba da cewa a rangadin aikin da suka gudanar, sun gano an sace rukuni 18 daga cikin rukunai 21 na fitilun kan titin, amma a halin yanzu ana aikin gyaransu.