Kasar Bangladesh, ta sanar da rage yawan kudaden da musulman ta zasu biya, don sauke faralin aikin Hajjin shekara mai kamawa wato 2025.
Kasar Bangladesh, na daya daga cikin kasashe masu yawan al’umma Musulmai a fadin duniya.
Wannan kokari yazo a daidai lokacin da ake zulumin cewa masu niyyar zuwa aikin Hajjin shekara mai kamawa daga Nigeria zasu biya kudaden da yawan su ka’iya kaiwa naira miliyan 10.
Hakan ya samo asali akan yadda gwamnatin tarayya ta cire tallafin aikin Hajjin.