Libya zata koro yan Nigeria dake zaune a kasar

0
38

Rahotanni sun tabbatar da cewa mahukuntan Libya sun shirya korar yan Nigeria mazauna kasar biyo bayan hukuncin da hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta yanke bayan rikicin kwallon kafar daya faru tsakanin Nigeria da tawagar kwallon kafar Libya.

Idan za’a iya tunawa a watan Oktoba ne tawagar Super Eagles ta Nigeria ta je kasar Libya don buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kafin Africa, amma mahukuntan Libya suka ki bawa yan Nigeria kulawa har hakan ya sanya suka shiga wani mawuyacin hali.

Haka ne yasa tawagar Super Eagles ta ki buga wasa da Libya tare da dawowa gida Nigeria ba tare da buga wasan ba.

Bayan haka Nigeria ta shigar da tawagar kwallon kafar Libya kafa inda aka ci Libya tarar Dala dubu 50.

Wannan hukuncin ya yiwa Libya ciwo inda suka daukaka kara.

Wani mazaunin Libya daga Nigeria yace zuwa yanzu an fara kama yan Nigeria a Libya, yayin da ya ke zantawa da jaridar Punch.

Kasar Libya na daga cikin Kasashen Afrika da yan Nigeria ke zuwa ci Rani.

Zuwa yanzu akwai dubban yan Nigeria dake rayuwa a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here