Wasu lauyoyi masu zaman kansu sun yi namijin kokarin ganin kananun yaran da gwamnatin tarayya ta gurfanar akan zargin yunkurin kifar da Gwamnatin, da tayar da tarzoma sun shaki iskar yanci.
Da fari anyi zaton cewa babu daya daga cikin yan arewa da zai kare yaran a gaban shari’a, sai dai an samu lauyoyi masu jajircewa, har suka tsayawa kananun yaran a gaban shari’a.
Karanta karin wasu labaran:Shugaban Nigeria ya nemi a ladabtar da jami’an tsaron da suka kama kananun yara lokacin zanga zanga
Bayan haka, yan arewa da sauran al’ummar kasashen duniya sunyi ala Wadai akan abun kunyar da gwamnatin tarayyar Nigeria tayi na cewa kananun yaran da basu kai shekara 18, zasu kifar da Gwamnati.
Idan za’a iya tunawa dai an kama kananun yaran kusan su 80, a jihohin Arewa lokacin zanga zangar yaki da yunwa data faru a ranar 1 ga watan Ogusta zuwa 10 ga watan.
An kama yaran da zargin daga tutar kasar Rasha.
Amman iyayen yaran sun ce ko kadan ‘ya’yan su basu aikata wannan laifi ba.
Lokacin da aka gurfanar da su Kotun Tarayya dake birnin tarayya Abuja, ta bayar da su beli akan naira miliyan 10 kowanne.
Bayan haka ne aka rika sukar gwamnatin har sai da mahukunta suka ce a saki kananun yaran.
Shugaban Nigeria Bola Tinubu, shine ya bayar da umarnin gaggauta sakin kananun yaran da aka kama a arewacin kasar lokacin zanga zangar neman shugabanci na gari da ta gudana a watan Ogusta.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ne ya sanar da hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa a ranar litinin.
A cewar Idris, Tinubu, ya bayar da umarnin sakin kananun yaran ba tare da bata lokaci ba, ko kuma jan kafa.
Tinubu, ya kuma bawa ma’aikatar jinkai ta kasa umarnin kulawa da walwalar yaran har a kai su ga iyayen su.
An kuma bayar da umarnin kafa wani kwamitin da zai bibiyi yadda aka tafiyar da lamarin kama yaran da yadda aka kula dasu a hannu jami’an tsaro.
Shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu, ya kuma bayar da umarnin bincikar jami’an tsaron da suka kama yaran.
Idan za’a iya tunawa an gurfanar da kananun yaran a gaban wata Kotun tarayya dake Abuja, da zargin cin amanar kasa, da kuma yunkurin juyin mulki a Nigeria, wanda kotu ta bayar da su beli akan naira miliyan 10 kowanne yaro daya.