Tsohon Daraktan Yakin Neman Zaben Obi/Datti, a zaben Nigeria na shekarar 2023, Doyin Okupe ya ce an yi alkawari cewa yankin Arewa zai mulki Nijeriya tsawon shekara takwas sannan yankin Kudu ya karba yayi shekara takwas.
Doyin Okupe ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga yankin Arewa ya yi shekara takwas a mulki, don haka Tinubu da ke kan mulki zai yi shekara takwas idan yana so.
Okupe wanda shine tsohon kakakin tsohon shagaban Nigeria Goodluck Jonathan, ya ce Tinubu na iya cin zaben shugaban kasa a 2027 idan ya iya shawo kan matsalolin da ke damun Nijeriya a yanzu.
A ya bayyana hakan yayin da ake hira da shi a gidan talabijin na Channels.Yace da Nigeria bata shiga wannan mawuyacin halin ba, watakila da kasar tuni durƙushewa.
Yace idan Tinubu ya magance matsalar man fetur da tsadar abinci kafin lokacin zabe yan Nigeria zasu sake zabar sa.