An kara farashin lantarki a Nigeria

0
13

Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki na Nigeria (DisCos) sun sanar da karin farashin wutar lantarki.

Wannan shine karin farashin lantarki na biyu cikin watanni hudu a kasar.Sabbin farashin, wanda zai fara aiki daga ranar Talata 5 ga watan Nuwamba, 2024, ya nuna yadda kowane kamfanin rarraba wutar lantarki zai sayar da wutar kamar yadda Hukumar Kula da farashin Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta tabbatar.

A cewar kamfanonin DisCos, farashin mita mai hawa daya ya tashi daga kimanin naira 117,000 zuwa naira 149,800, ya danganta da kamfanin da ke raba wutar a yankin da kuma masu sayar da mitoci.

A jihar Kano, mita mai hawa daya, farashin ta yana tsakanin Naira 127,9925 zuwa Naira 129,999.75, sai kuma mita mai hawa Uku, tana tsakanin Naira 223,793 zuwa Naira 235,425.

A jihar Kaduna kuwa, mita mai hawa daya farashin yana tsakanin Naira 131,150 zuwa Naira 142,548.94 yayin da Mita mai hawa Uku ke tsakanin Naira 220,375 zuwa Naira 232,008.04.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here