Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta kammala rabon kayan aikin zabe masu muhimmanci da za’a yi amfani da su a zaben gwamnan jihar Ondo na ranar asabar mai zuwa.
Kwamishinan hukumar zaben ta kasa reshen jahar Ondo Oluwatoyin Babalola, ne ya sanar da hakan lokacin da yake sanya idanu akan yadda aikin rabon kayan ya kasance, a babban bankin kasa dake jihar.
Karanta karin wasu labaran:::Sojoji sun kori mayakan Lakurawa daga sansanin su na Kebbi
Yace zuwa yanzu an bawa kowacce karamar hukuma kayan aikin zaben, wanda jihar ke dauke da kananun hukumomi 18.
Babalola, yace rabon kayan da aka fara akan lokaci ya bayyana yadda suka shiryawa gudanar da zaben kamar yadda aka tsara, cikin inganci da gaskiya.
Yace anyi rabon cikin kwanciyar hankali kuma babu wata karamar hukumar da ba’a bawa kayan zaben ba.
Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa wakilan jam’iyyun siyasar da zasu shiga zaben sun halarci wajen rabon kayan zaben, tare da manyan jami’an tsaro.